Labaran Alajabi

ABIN TAUSAYI: Sojoji Abokan Aikin Mahaifinta Da Ya Rasu Sun Halarci Walimar Saukar Kur’ani Da Ta Yi….ba ita ce sojan ba, mahaifinta da ya rasú ne Sojań amma…

Wannan yarinya dai sunan ta Amina, mahaifinta ne soja, amma ya gamu da ajalin sa a filin daga yayin kare martaban ƙasa shekara goma da suka gabata a Maiduguri.

Amina ta yi saukar Kur’ani a ƙarshen makon da ya wuce. Jin haka yasa waɗannan abokan aikin mahaifin nata suka taso domin su share mata raɗaɗin rashin ganin mahaifin nata a wannan rana.

Sun zauna tun daga farkon taron har zuwa ƙarshen sa, sun kuma yi nasiha da jan hankalin matasa maza da mata.

Daga ƙarshe sunyi alƙawarin za su dinga tallafawa da kuɗin karatun yaran abokin nasu.

Allah Ya saka musu da alkairi.

Don Allah idan ka ji ɗaɗin wannan labarin ka yada (sharin) domin jama’a su gani su yi koyi da waɗannan sojojin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DANNA NAN KAGANI