SHEIK AHMAD TIJJANI GURUNTUM: “Kodai Malam Shine Magajin Sheik Ja’afar Ta Fuskar Iya Sarrafa Harshe? Shiga kaji abin mamaki👇
Idan Allah Yayi maka baiwa kagode masa, sai kuma Allah YaÆ™ara maka, É—aya daga cikin ni’imar da Allah yayiwa arewa A yanzu akwai manyan malamai masu gogayya da manyan malaman duniya, acikin masu baiwar aika saÆ™o cikin hikima da misali abin Burgewa akwai Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
Tabbas Munyi kewar manyan malamai irinsu sheik Ja’afar, albani, sheik bamba da sauransu, amma babbar baiwar da Allah yayi sheik Ja’afar akwai iya sarrafa harshe, wanda a yanzu babu wanda yake kwatanta sarrafa harshen Hausa da lafazi mai sauÆ™in ganewa irin sheik Guruntum.
Ana yiwa malam Guruntum laÆ™abi da “likitan zuciya” kokuma kaji ana cewa injiniyan gyaran zuciya, shine malamin da zaka riÆ™a jin karatunsa amma har baka so azo Æ™arshe.
Akwai wani misali da malam yabayar cikin wani karatu, inda Malam Yace “Man Sagir, Daga Sanda Mutum Ya Shekara Arba’in, Hamsin ko Sittin, Lahira Ko A Ƙasa Ake Zuwa Ai Ya Kusa Kai Wa .”
Sai Kuma Inda yake bada misalin Cewa “Zakaga akwai makarantar kuramai a Garinku Kai a zatonka kullum ‘yayan wasu Za’a rinqa kaiwa makarantar, Ina ai idan kayi haka ai bakasan waye Allah ba, Dole kasa a ranka indai har kana haihuwa to kaima watarana zakai naka Dan makarantar”
Wannan misali ne wanda kowanne irin mutum zai gane, kuma dole zai girgizashi (komai ƙarancin fahimtar mutum).
Ko zaka iya tuna wani misali da malam Yabayar?
ALLAH YA KARAWA MALAM LAPIYA DA NISAN KWANA🥰🤲