Labaran Duniya
BA IYA ƳAR FIM BA, ZAN IYA AUREN KARUWA MA WACE TA KAMA DAKI TAKE KARUWÀNCIŃ, CEWAR JARUMIN KANNYWOOD BABA SADIQ KARIN BAYANI👇
A cewar jarumin, ba a duban halin da ake ciki gaba ake dubawa dan haka ba ma ƴar Fim kaɗai ba matar da ta kama ɗaki a gidan karuwai ma take karuwanci idan ta daina zai iya aurenta ya zauna da matarsa.
Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito Baba Sadik wanda aka fi sani da Lukman a fim ɗin Kwana Casa’in kana tauraro cikin shirin “Labarina” na bayyana haka ta cikin wani bidiyo da aka zanta da shi. Kamar yadda ya ce:
“Abin da ya wuce ba shi ne abin dubawa ba, gaba ɗayanmu muna kallon gaba ne ba baya ba, dan haka zan iya auren ƴar fim, ba ma ƴar fim kawai ba har karuwa ma zan iya aura idan ta tuba”. A cewarsa.