Labaran Duniya

RA’AYÍ: Shin Da Wace Irin Doka Akewa Mabiya Malam Zakzaky Húkunci A Najèriya Ne, Cewar Wani Babban Lauya A Kasar Karin bayani..👇

Nayi mamaki irin yadda naga mabambantar ra’ayoyi akan haadisañ data faru a Zaria da Kaduna tsakanin Yan Shi’a mabiya Sheikh Zakzaky da jami’an tsar0n Najeriya wacce tayi sanadin ra$a rayúka da samun munanan raunúka daga bangaren mabiya Sheikh Zakzaky. Abun da ya fi bani mamaki shine yadda wasu lauyoyi suke ganin ahliyya ko shar’iyyar ki$an Yan Shi’a sab0da suna zagin Sahabbai da matan manz0n Allah (SAWW).

Ina wannan rubutun ne a matsayina na lauya saboda haka ina kallon abun ne ta mahangar shari’a matsalar zagin Sahabbai matsalace k0 ince tuhuma ce aqa’idiyya wacce shekaru fiye da dari bakwai ana tattauna ta a majaloli na ilimi daban daban tsakanin malamai wanda a zauren karatu ne kawai za’a iya hallale matsalar ba’a titi ko a soshal midiya ba.

Muqaddara Yan Shi’a suna zagin Sahabbai da matan Manzan Allah (S.A.W.W.) wanda wannan tuhumar Yan Shi’ar sun dade suna musantata. Mu qaddara cewa suna zagin Kuma hukuncin zagin shine kisa. In dai da dokokin Najeriya za’a yi musu hukunci kamasu za’ayi sannan a gurfanar dasu a kotu in kotu ta samesu da laifi shine za’a kashe su. Dan neman karin bayani za’a iya duba sashi na 33 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 sannan za’a iya duba shari’ar da kotun koli tayi tsakanin Nasiru Bello da Attorney General na Jahar Oyo zaka Ga yadda a qayyama rai.

Qa’ida itace kowa ne matuhumi bari’un ne akan tuhumar da ake masa (wato duk wanda ake tuhuma da aikata wani laifi ana kallon sa kamar bayyi bane) har sai mai tuhuma ya tabbatar da tuhumar sa. Sashi na 139 na kundin tafi da sheda na Najeriya na 2023 cewa yayi nauyin tabbatar da da’awa ko tuhuma tana wuyan mai tuhuma ne kuma sashi na 36 (5) na kundin tsarin mulkin Najeriya shima abun da ya tabbatar kenan bugu da kari malam Mai Tuhufah da sauran Malamai na musulunci suma maganar su kenan nauyin tabbatar da da’awa tana wuyan mai tuhuma ne.

Mutum Dan uwanka ne ko’a mutuntaka ko’a imani. Saboda haka a qa’ida ta Dan Adamtaka ko’a idan doka kuskure ne kashe rai ba tare da bin matakai ta shari’a ba wannan ran na musulmi ne kona kirista kai koda ran wanda bai da addini ne saboda a idan dokar Najeriya rai baifi rai ba kuma kuma sashi na 38 da 39 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bawa kowa damar yin addini da yake so ba tare da an nuna masa bambanci ba.

Akan wadannan usus din justifying ki$an da akawa mabiya Sheikh Zakzaky da zagin Sahabbai ko matan Manzan Allah (SAWW) fakewa ce da guzuma a Harbi karsana masu irin wannan maganar in sun samu dama zasu kashe dan Shi’a wasa’un yayi zanga-zanga ko baiyi ba saboda kawai ya saba musu a fahimta Kuma shi bashi da damar yin tasa fahimtar. Saboda kiyayyace ta gado. Kira na ga masu da’awar Yan Shi’a suna zagiñ Sahabbai in har da gaske kuke ana zagin, kuma kunsan masu zagin, kuma zagin laifi ne, kuma hukuncin zagin shine kisa kuma ku masu bin doka ne. kuyi korafi mana ga hukumomi tunda kotunan da za’a kai Yan Shi’an babu Yan Shi’a a alkalan za’a hukunta Yan Shi’a yanda kuke so.

Allah Yana karanatar damu a cikin Alqur’ani Mai girma a sura ta biyar aya ta bakwai inda yake cewa kada kiyayyar da kakewa wani mutum ya rufe maka ido ka kasa masa adalci. Ina bawa duk wanda wannan rubutun nawa ya batawa rai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DANNA NAN KAGANI