Labaran Duniya

Abin mamaki shi ne yadda Al’ummar Ƙasar Nijar suka gudanar da zanga-zangar neman sojojin Amerika du fice musu daga ƙasa Akwai Kari bayani👇

Da wannan zanga-zangar ne suka kori sojojin Faransa daga ƙasar su a watannin bayan, ba addu’a suka tsaya yi ba, ‘Su ce Allah bamu Son Faransa, Allah ka kore mana Faransa daga kasar mu’. Ba haka suka yi ba, fitowa suka yi, sun ɗauki kusan kwanan uku ajere, sun mamaya kofar ofishin jakadacin Faransa, babu zagi, babu ƙone-ƙone, cewa suke Faransa su fice musu daga ƙasa.

Sai dai abin mamaki duk yawan Manayan Malaman dake kasar Nijar, bani ji wani Malamin da ya fito ya ce yin zanga-zanga Haramun ne a Musulunci ba.

Amma a nan Nijeriya Malamin wa’azin Turmi sun ce yin Zanga-zanga domin neman ‘Yanci da bayyana zaluncin azzaluman shugabanni Haramun ne inji su.

Shin Malaman Hausawa masu Wa’azin Turmi, sune suka fi duk Malamai sanin hukuncin shari’a ko kuwa dai kawai suna ƙare Miyar Gidansu ne a wurin azzaluman shugabani, ko kuma tsoron mutuwa suke yi?

Almujtaba Abubakar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DANNA NAN KAGANI