Labaran Alajabi

NA KAMU DA ƘAUNAR SHEIHK YUSUF ASSADUSSUNNAH BA ZAN IYA RAYUWA BA IDAN BABU SHI, CEWAR JAMILA NASIDI KARANTA ƘARIN BAYANI

Wata matashi mai suna Jamila Nasidi, ta shaidawa Jaridar Dokin Ƙarfe TV cewa, tana son fitaccen Malamin Addinin Musuluncinnan Sheíkh Yusuf Assadussunnah kuma a shirye take ko gobe a ɗaura musu aure matuƙar ya yarda zai aure ta.

A cewar ta “Allah Ya jarabce ni da ƙaunar Sheíkh Yusuf Assadussunnah, ba zan iya rayuwa ba in babu shi. Na kamu da ƙaunarsa ne saboda shi mutum ne mai tsananin tsoron Allah da faɗar gaskiya”. A cewarta.

Jamila ta kuma ƙara da cewa “Saboda tsananin ƙaunarsa da nake, idan wasu sun mun magana muryarsa nake ji a cikin zuciyata. Idan ina barci hasken fuskarsa nake gani. Idan zai aure ni zan yafe masa lefe da sadaki ko gobe ya turo a ɗaura mana aure”. Cewar Jamila Nasidi.

Wane fata zaku yi mata?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DANNA NAN KAGANI