Labaran Duniya

NA KAMU DA ƘAUNAR AHMED MUSA, WALLAHI INA SON SA FIYE DA YADDA NAKE SON RAYUWATA, CEWAR HALIMA IBRAHIM ƘARIN BANI..

Wata matashiyar budurwa ta bayyana cewa ta kamu da matsananciyar ƙaunar fitaccen ɗan ƙwallon ƙafan Najeriya, Kaftin ɗin ƙungiyar Super Eagle, Ahmed Musa. Kuma soyayyar da take masa soyayya ce ta tsakani da Allah irin wadda ba ta taɓa yi wa wani ɗa namiji irin ta ba a rayuwarta.

Halima ta bayyana haka ne ta cikin wata tattaunawa da Jaridar Dokin Ƙarfe TV, inda ta ƙara da cewa “saboda ƙaunar da nake yi wa Ahmed Musa na yi Umrah da Nafilfili cikin dare na yi addu’a na roƙi Allah cewa idan ba alkhairi bane a gare ni ko soyayyata za ta zama cutarwa a gare shi Allah Ya fidda mun shi na manta shi a rayuwata amma sonsa ƙaruwa yake yi har yanzu a zuciyata”. Ta ce.

Halima ta cigaba da cewa “Ina son Ahmed Musa fiye da rayuwata ko da zai rasa komai nasa a Duniya zan iya rayuwa da shi rayuwa ta har abada, kuma zan iya sadaukar da komai na rayuwata a kansa”. In ji ta.

Ta cigaba da cewa saboda soyayyar da nake yi wa Ahmed Musa, nayi addu’o’i da karatun ƙur’ani cikin azumi da manufar Allah Ya ba shi ladan ya kare shi daga magauta. Kullum sai na yi masa addu’a Allah Ya kare shi daga sharrin maƙiyansa na fili da na ɓoye”. In ji Halima.

Daga nan ta ƙara da cewa “Na fi son rayuwar Ahmed Musa a kan tawa, na zaɓi na mutu shi ya rayu. Idan son da nake masa ba na tsakani da Allah ba ne ka da Allah Ya sa na shiga Aljannah”. Cewar Halima Ibrahim.

Wane fata zaku yi mata?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DANNA NAN KAGANI