Labaran Alajabi

ADA KALLON MAHAUKACI NAKE YI WA SAURAYINA IDAN YA CE MUN ZA TA FASHE AMMA YANZU NA YI DA-NA-SANI, CEWAR HANAN JARUMA KARANTA ƘARIN BANI..

Wata matashiyar budurwa mai suna Hanan wacce aka fi sani da jaruma ta shaidawa Jaridar Dokin Ƙarfe TV cewa ada kafin (Notcoin) ya fashe kallon mahaukaci take yi wa saurayinta dake Mining idan ya ce mata za ta fashe amma yanzu ta yi da-na-sani da ta ga ta fashe ɗin.

“Kullum saurayina yana ce mun za ta fashe, ko buƙatuna na kawo masa ko in muna hira a waya cewa yake za ta fashe in ta fashe zai ba ni duk abin da nake so amma ni kuma kallon mahaukaci nake masa sai yanzu da ta fashe nake da-na-sani”. Ta ce.

Hanan ta ƙara da cewa “yanzu haka ya turo min kyautar kuɗi Naira 500,000 cikin Account ɗina. Kuma yana nema na zai ƙara ba ni kyautar sabuwar waya Iphone14 amma naƙi yarda mu haɗu saboda kunyarsa nake ji sakamakon kallon mahaukaci da nayi masa a baya. Ina neman shawarar al’umma na karɓi kyaututtukan da zai ba ni ko kar na karɓa ?”. Cewar Hanan Jaruma.

Wace shawara zaku bata?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DANNA NAN KAGANI