Labaran Duniya
Wane Fata Zaku Yiwa Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi ll ? bayan majalisar dokoki ta Kano ta….
YANZU – YANZU: Majalisar Dokokin Kano Ta Amince A Sake Yi Wa Dokar Masarautu Gyara
Majalisar tace a dawo da dokar domin duba ta tsaf dalla-dalla domin gyara wasu abubuwa dake ciki
Idan baku manta ba dai a zamanin Ganduje anyiwa dokar kwaskwarima tare da samar da ƙarin masarautu 4, inda aka karkasa masarautun Kano zuwa gida 5
Ko a kwanakin baya wasu kungiyoyi sunyi kira da ai gyara kan dokar domin dunkule masarautun Kano su zama ɗaya, tare da neman a cire Sarkin Kano na yanzu tare da maye gurbin sa da Sarkin Kano na 14 Khalifa Muhammad Sunusi ll.
Tuni dai majalisar ta amince a maido mata dokar domin duba ta.
Meye fatan ku kan wannan yunkuri na majalisar?