Tofa. Ko Mala’iku ne suka sauko suka taya mu addu’a babu abinda ze canza a Arewa. Hujjar da Karin bayani👇
Addu’a ba za ta taÉ“a gyara halin da Arewacin Najeriya ke ciki ba! Na yarda da Allah kuma na yarda da addu’a. Amma Walalhi ko Mala’iku zasu sauko daga sama su taya mu addu’a babu abinda zai gyaru. Har Saudiya da Iran Æ™asashen Musulmi 2 mafi yawan Æ™arfin faÉ—a aji da kuma girman Aqidu har a can ana zanga-zanga ga hukuma ta hanya daban-daban, babu mamaki wani yaji maganan tayi girma ko tayi zafi! Amma hakan take gaskiya!. Ra’ayi na ne wannan kuma bazanyi wani Æ™arin haske ba.
Dole sai mutane sun matsa kafin a san suna nan. Dole ayi musu abinda basa so, dole ayi zanga-zanga, dole ayi tawaye gare su kafin su gyara, ba kuga misali ba, ai abinda Mallam Aminu Daurawa yayi sunan shi tawaye, wani nau’i ne na zanga-zanga amma me sauÆ™in ciki, to Mallam shi É—aya kenan ina kuma ace Miliyoyin jama’a zasuyi nasu salon wallahi cikin kwanaki komai zai canza! Shin jama’a ba zaku hankalta ba?
Duk garuruwan da sukayi zanga-zanga suka tashi tsaye, musamman kudancin Najeriya yanzu haka sun fara ganin canji, wanda kuma suka ki saboda fatawar Miyagun Mallamai, babu canji sai satar abinci da tare motoci haka za’ayi tayi babu wani cigaba sai tarin matsaloli. Na sha faÉ—a wallahi ba domin Miyagun Mallamai ba da Najeriya (Musamman Arewa) ta gyaru tayi Æ™yau. Malaman da suka yarda a fasa shagunan mutane a saci abinci amma kar ayi wa gwamnati zanga-zanga!. Tirrr.
—Bilya Hamza Dass