Wasu Fusatattun Matasa Sun Kashe Wani Matsahi Mai Suna Bello, Har Lahira Akan Budurwa saboda tace…
Lamarin ya faru ne a jiya alhamis da missalin karfe 4 na yamma, sakamakon neman budurwa data hadu su tsakanin abokan.
Anyi jana’izar marigayin ne a jiya alhamis a kofar mai martaba hakimin Hashidu Alh Abubakar Adamu da missalin karfe 5 na yamma, yanzu haka matasan da suka aikata wannan aika-aika sun gudu, wasu daga cikin abokan marigayin kuma sun jikkata suna kwance a gadon asibiti.
Al’ummar yankin sun yi kira ga Gomnatin jihar Gombe data dauki babban mataki akan su domin kaucewa faruwar hakan a gaba, haka zalika sun sake kira ga gomnati da tayi kira ga sarakuna dasu dauki mataki kan matasan da suke yin shagalin buki (party) domin wasun su suna tada zaune tsaye tsakanin al’umma musamman mutanen ƙauyuka.
Hakan barazana ce ga zaman lafiya a jihar Gombe kuma hakan shine yake jawo wasu asarar rayuka musamman matasa, saboda matasan suna yawo da makami yayin bukukuwa koda biki bai shafe su ba su kan iya shiga bukin domin su tada zaune tsaye wajen bukin.