Kuncin Rayuwar zawarci shike jefa Dayawa Daga Zawarawa fadawa cikin karuwanci dom..
Daga Zainab Giwar Matan Gona
Zawarci yana da daci a zukatan zawarawa, Nayi Nazari Akan Mata Da Maza wallahi da rayuwar zawarci gara Jinkirin Aure Ga Budurwa.
A Gidajen Talakawa kuncin Rayuwar zawarci Shike jefa dayawa daga zawarawa Fadawa cikin Karuwanci don nemawa Kansu abin biyan buƙatar Rayuwa.
A Lokacin da Mace takasance Bazawara a cikin gidanSu kannenta zasu Rinqa Yimata kallon Hadarin Kaji, kuma ta samu ƴan cin yawo guri-guri domin a Lokacin da kowa bane zai Iya tsawata Mata ba.
Manzon Allah (s w s) Yace “Ku Tausayama Wanda Yayi Arziki Amma Arzikin Yaqare”
Don Haka yakamata mu tausayawa Zawarawa.
Shin!! Wai Mike Jefa Mata A Rayuwar Zawarci?
1•Rashin Bincike Kafin Aure:
2 •Wani dan shaye-shayene
3 •Wani dan caca ne
4 •Wani baida hakuri
5 •Wani barawone.
6 •Rashin Haquri:
7 •Wata Rashin son zama da Kishiya
8 •Wata Yawan Gulma
9 •Raina miji.
10 •Wasu Kuma Mazanne Masu Auri Saki.
11 •Wasu Kuma Mutuwace Ke Yanke
Kaunar. ALLAH ka tsare muna imaninmu da mutuncinmu da addininmu ALLAH kasa mufi karfin zuciyoyinmu kabamu ikon hadiye kwadayinmu kada kwadayi ya hade mu.
Ya Allah ka raba mata daga fadawa
rayuwar Zawarci da kuma karuwanci.
✍️ RUBUTAWA
Zainab Musa Ya’u
(Gimbiya) Giwar Matan Gona.