ZAN SAYI RUWA MOTA 50 NA RABA A UNGUWANNIN DA SUKA FI RASHIN RUWA A BIRNIN KANO, CEWAR JARUMAR KANNYWOOD A’ISHA HUMAIRA Karanta Karin bayani
Jaruma a masana’antar Kannywood A’isha Humaira ta bayyana cewa za ta sayi mota 50 ta ruwa ta raba a unguwannin da ke fama da matsananciyar matsalar rashin ruwa a birnin Kano a daidai lokacin da jama’a ke kokawa.
Jaridar Dokin Karfe TV ta ruwaito Jarumar na bayyana haka a shafinta na Instagram kamar yadda ta ce:
“Na ji ana fama da matsalar rashin ruwa a cikin gari, dan Allah ku taimaka ku bayyana unguwannin da suka fi rashin ruwan zan sayi kamar mota 50 saboda Allah”. A cewarta.
Jarumar ta kuma ba da motocin ruwan guda goma-goma ga mata masu ƙungiyoyin agaji; Fauziyya D. Suleiman da Mansura Isah domin su raba wa al’umma daga cikin mota hamsin ɗin da ta tsara saya. Sannan ta kuma ƙara da cewa wannan tallafi ya shafi iya al’ummar dake cikin birnin Kano ne. Kamar yadda Jaridar Dokin Ƙarfe TV ruwaito.