Labaran Duniya

Jama’a Don Allah Ina Cigiyar Mahaifina, Sama Da Shekaru 37 Kenan Babu Labarinsa.. 👆

Daga Comrd Amina Yahaya Salisu

Assalamu alaikum ;;
Masu yawan tambaya ta ta inbox mai ya sa nake yawan posting din mutanen da suka bata, da masu zuwa yi min godiya bayan an samu wanda ya bata; to yau zan gaya muku dalilina.

Ni ma hakan ya faru da ni, (victim ce) na san radadin batan naka, wani ciwo ne wanda ba ya taba warkewa, mutum zai rayu ne kullum a tunanin nashi ko a mace ko a raye ko zai dawo ko ba zai dawo ba.

Mahaifina ya bata tun ina yar shekara 2 zuwa uku, sunan sa Alh Yahaya Salisu.

Kafin tafiyar sa shi mazaunin anguwar Sheka gidan zoo ne a Kano ya bar mata uku, ‘ya’ya goma sha biyar, ya bar Kano da niyyar zuwa Lagos, amma sai ya wuce zuwa Bauchi gurin kaninsa, daga nan ya kaiwa babbar yayar mu ziyara a makarantar BACAS ya yi mata sallama, tun daga ranar ba a sake jin balarin sa ba har rana mai kamar ta yau.

Ina neman alfarmar ku da ku taya ni sharing ko Allah zai sa ni ma in dace da wanda ya taba koda ganin sa ne.

Allah Ya sa muna da rabon ganawa da shi amin, idan kuma ya rasu Allah Ya jikan sa da rahama amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DANNA NAN KAGANI